in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta mika hanyar mota da ta gina ga gwamnatin Saliyo
2014-04-27 17:32:59 cri

Ranar 26 ga watan nan na Afrilu ne jakadan kasar Sin da ke Saliyo Zhao Yanbo, ya mika hanyar mota da kasar Sin ta taimaka wajen ginawa ga hannun gwamnatin Saliyo a hukumance.

An dai gudanar da bikin mika hanyar ne a garin Regent da ke kusa da birnin Freetown, hedkwatar kasar ta Saliyo.

Hanyar wadda ke da tsawon kilomita 11.26, ta hada garin Regent da garin Kosso, za kuma ta baiwa mazauna birnin Freetown damar saduwa da sauran yankunan kasar cikin sauki. Tare da rage matsalar cunkuson ababen hawa a birnin.

Yayin wannan bikin shugaba Ernest Bai Koroma na Saliyo, ya bayyana cewa, a 'yan shekarun nan gwamnatin Sin da kamfanonin kasar, sun himmatu wajen inganta ayyukan more rayuwar mazauna birnin Freetown. Don haka ya bayyana godiyarsa game da wannan muhimmin aiki na kyautata rayuwar al'umma bayan kammalar yakin basasar kasar.

A nasa bangare Zhao Yanbo, ya ce Sin da Saliyo sun samu sakamako mai kyau a fagen hadin gwiwa a fannonin ayyukan more rayuwar jama'a, da kiwon lafiya, da ilmi, da horas da kwararru da dai sauransu.

Daga nan sai ya yi fatan wannan hanya ta zamo jigon samun wadata, da bunkasuwar tattalin arzikin al'ummar kasar ta Saliyo. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China