Ministan harkokin wajen kasar Sin Mista Wang Yi, ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Saliyo Mista Samura Kamara, wanda yake ziyarar aiki a nan kasar Sin.
A gun shawarwarin, Mista Wang ya bayyana cewa, duk da irin bunkasuwar da kasar Sin ta samu, har abada za ta kasancewa abokiya kuma kawa ga jama'ar kasashen dake nahiyar Afirka, wadanda suka amince da ita.
Wang ya ci gaba da cewa, kasar Sin tana kan kokari tare da kasar Saliyo, wajen ingantan aminci a fannin siyasa, da sa kaimi ga hadin kai da ka iya samar da moriya ga bangarorin Biyu, da kara cudanyar al'adu, ta yadda za a iya samun bunkasuwar Sin da Afirka tare.
Mista Kamara ya bayyana cewa, Saliyo ta dauki kasar Sin a matsayin wata muhimmiyar abokiyar hadin gwiwa, kuma tana godiya ga kasar ta Sin, bisa taimakawa Saliyon da take yi, wajen samun zaman karko, da sake gina kasa cikin dogon lokaci.
Ya ci gaba da cewa, Sin ta riga ta zama wata abokiya bisa manyan tsare-tsare, a fagen taikamawa Afirka don ta samu dogaro da kanta, har kullum Afirka na bude kofa ga Sin, don hada kai tsakanin bangarorin biyu a dukkan fannoni.
Ban da wannan kuma, Mista Kamara ya soki wasu 'yan ta'adda, wadanda suka kaddamar da wani harin ta'addanci a nan birnin Beijing a 'yan kwanakin baya.(Danladi)