Jiya Laraba 12 ga wata, kwamitin sulhu na MDD ya yanke kudurin tsawaita wa'adin ofishin kula da zaman lafiya na MDD dake kasar Saliyo har zuwa ran 31 ga watan Maris na shekarar 2013.
Kudurin kuma ya yi kira ga gwamnati, jama'a, kafofin yada labaru, jam'iyyun siyasa da magoyansu na kasar Saliyo da su ci gaba da kawo yanayi mai kyau da zai taimaka wajen yin zabe cikin lumana yadda ya kamata, tare kuma da cigaba da yin shawarari tsakanin bangarori daban-daban, ta yadda za a kawar da bambancin ra'ayi, da kuma mutunta sakamakon zabe.
Dadin dadawa, kudurin ya nemi ofishin wanzar da zaman lafiya na MDD dake kasar Saliyo da rukunin kasa da kasa na MDD da kasashen duniya su hada kansu su ci gaba da ba da taimako ga gwamnatin kasar Saliyo, da hukumomin diplomasiyya da tsaron kasar, ta yadda za a gudanar da zabe yadda ya kamata.
An ba da labari cewa, an kafa wannan ofishi a shekarar 2008 bisa iznin kwamitin sulhu, wanda wa'adinsa zai cika a ran 15 ga wannan wata. Kuma, kasar Saliyo za ta yi babban zabe a watan Nuwanba na bana.(Amina)