A shekara ta 1996 ne Kabbah ya hau karagar mulkin kasar Saliyo. Kama madafun ikon da ya yi, ya kawo karshen shekaru goma na mulkin dakarun sojoji na kasar ta Saliyo.
Wani juyin mulki da aka yi a shekarar 1997 ta yi sanadiyyar saukarsa daga kan mukamin shugaban kasa na dan wani lokaci, kuma daga baya sai ya koma matsayin shi na shugaban kasa a shekarar 1998, tare da taimakon rundunar shiga tsakani ta sojin kasashen Africa ta yamma.
Shi dai tsohon shugaban kasar ta Saliyo ya samu nasarar jagorar kasar wajen shirin samar da zaman lafiya tare da kawo karshen yaki a kasar ta Saliyo a watan Janairu na shekarar ta 2002.
A shekarar ta 2007 dai ne Marigayi Kabbah ya yi ritaya daga harkokin siyasa bayan da ya yi shugabancin kasa har karo na biyu. (Suwaiba)