in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban kasar Saliyo
2013-06-26 21:06:37 cri

A ranar 26 ga wata a nan birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban kasar Saliyo Ernest Bai Koroma da ke halartar taron tattaunawa kan zaman lafiyar duniya karo na biyu a kasar Sin.

A lokacin ganawar Shugaba Xi ya bayyana cewa, ana kiyaye zaman lafiya da bunkasuwar tattalin arziki a kasar Saliyo cikin shekaru da dama da suka wuce, abin da ya bayyana cewa, ana samun ci gaba a dukkan nahiyar Afirka, don haka Sin tana farin ciki da ganin hakan.

Kasar Sin, in ji shi tana fatan kasar Saliyo za su cimma manufar samun wadata cikin hanzari, kana tana goyon bayan kasar Saliyo wajen inganta aikin ba da ilmi, kiwon lafiya da dai sauransu, har ma da taimakama Saliyo don ganin manyan kamfanonin Sin dake kasar sun hada gwiwa da Saliyo a fannonin ayyukan more rayuwa, ma'adinai, sadarwa, aikin noma da dai sauransu. A saboda haka kuma Sin ta bukaci kamfanonin da su gudanar da ayyukansu bisa doka, da bada gudummawa ga zaman al'ummar kasar Saliyo.

Shugaba Xi ya kuma bayyana cewa, Sin da Afirka na tafiya kafada da kafada, don haka za su iya hadin gwiwa a fannoni daban daban, domin samun makoma mai haske. Ya kamata Sin da Afirka su zama aminai na dindindin, da kuma ingiza dangantakar abokantaka a tsakaninsu ta sabon salo bisa manya tsare-tsare, domin amfana jama'ar kasashen biyu.

A nasa bangaren ,Shugaba Ernest Koroma ya bayyana cewa, shugaba Xi ya zabi Afirka ta zama zangon farko na ziyararsa bayan darewarsa karagar mulkin kasar Sin, abin da ya sa kaimi ga ci gaban dangantaka a tsakanin Sin da Afirka, da kuma kara kwarin gwiwar kasashen Afirka da jama'arsu sosai.

Shugaban ya mika godiyar kasar Saliyo ga kasar Sin bisa ga goyon baya da taimakon da take bayarwa, sannan kuma tana son inganta hadin kansu don samun wadata tare. Ya ce Saliyo za ta ci gaba da kyautata yanayin zuba jarinta, sannan tana maraba da yawan masana'antun kasar Sin wajen raya ayyukansu a kasar don moriyar juna.(Zainab, Kande)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China