in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Boko Haram ta dauki alhakin harin Bam a Abuja
2014-04-20 16:03:26 cri
Kungiyar Jama'atu Ahlussunnah Lidda'awati wal-Jihad, wadda aka fi sani da Boko Haram, ta dauki alhakin kai harin da ya hallaka mutane a kalla 75 tare da jikkata wasu da dama.

Wani faifan bidiyo da kungiyar ta fitar, ya nuna shugaba ta Abubakar Shekau na cewa su ne suka kai harin na tashar motar Nyanya dake wajen birnin tarayyar Najeriyar a ranar Litinin din da ta gabata.

Tun daga shekarar 2009 kawo yanzu, kungiyar ta Boko Haram na ci gaba da kasancewa babbar barazana ga tsaron rayukan al'ummar Najeriya. Ta kuma kaddamar da manyan hare-hare da dama, musamman a jahohin Borno da Adamawa da Yobe, wadanda ke arewa maso gabashin kasar.  (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China