Hukumar kula da gidajen kurkuku ta kasar Isra'ila ta bayar da rahoto cewa, bisa yarjejeniyar musayar fursunonin da gwamnatin Isra'ila da kungiyar Hamas suka kulla, an ce, za a saki fursunoni 477 'yan Palesdinu na matakin farko, wadanda suka hada da maza 450 da mata 27, kuma za a kai su zirin Gaza da yammacin gabar kogin Jordan da birnin Kudus ta gabas da kuma Isra'ila ko da sauran kasashen waje.
Majalisar ministoci ta kasar Isra'ila ta zartas da yarjejeniyar musayar fursunonin tare da kungiyar Hamas a ran 12 ga wata.Bisa wannan yarjejeniya, kasar Isra'ila za ta saki fursunonin 'yan Palesdinu 1027 da take tsare dasu a gidajen kurkukun ta domin musayar wani sojin Isra'ila Schalit.(Lami)