Xia Guang ya ce, halin da kasar Sin ke ciki wajen kiyaye muhalli yana inganta, amma ana fuskantar matsanacin hali game da ingancin ruwa, da na teku, gami da na iska. Ya jaddada cewa, ya kamata a kara kyautata batun kiyaye muhalli a kasar Sin.
Game da matsalar da kasar Sin ke fuskanta a kasar, a gun cikakken zaman taro na 3 na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18 da aka kammala a watan jiya, an fidda sabuwar manufar kiyaye muhalli mai tsauri, ta yadda za a kiyaye muhallin halittu a kasar.(Bako)