in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci kasashen Afrika dasu yi kokarin raya tattalin arziki tare da kare muhalli don samar da isassun abinci
2014-03-03 21:10:56 cri
Shirin kiyaye muhalli na MDD a yau litinin 3 ga wata yayi kira ga kasashen Afrika da su yi kokarin raya tattalin arziki tare da kare muhalli domin samar da isassun abinci a nahiyar.

Da yake Magana wajen bikin ranar muhalli na Afrika da kuma ranar Wangari Maathai a Nairobi,Babban jami'in shirin kula da muhalli na MDD Achim Steiner ya lura da cewa a yanzu haka an riga an fitar da hanyoyi inganta ayyukan noma da kare muhalli da kuma Karin hanyoyin inganta tattalin arziki a nahiyar baki daya.

Don haka inji shi wadannan hanyoyin ya kamata a kara azama don ganin an cimma haye dukkan kalubalolin da za'a fuskanta da suka hada daga sauyin yanayi zuwa rashin kyaun kasan shuka da nahiyar ke fuskanta.

Fiye da matasa 200 da manyan masana suka hallara a Nairobi a litinin din nan domin nazari akan manyan batutuwa da suka shafi yanayi da suka shafi Afrika wadanda suka hada da farautar namun daji ba bisa ka'ida ba,sare itatuwa da kuma barazanar karancin abinci.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China