in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hakikance yawan albarkatun muhallin Afrika shi ne ginshikin ingiza cigaba
2013-12-05 10:36:14 cri

Ya kamata kasashen Afrika su aza tushen tattalin arziki bisa albarkatun muhalli, har ma da dazuzzuka, filayen noma, tsabtattun ruwa sha, ciyayi domin daidaita cigaban dake tafiya da kare muhalli, in ji shugaban hukumar kula da tsarin kare mullahi ta MDD (PNUE) a ranar Laraba. Darektan zartaswa na PNUE, Achim Steiner, ya yi kira ga gwamnatocin kasashen Afrika da su hada kididdigar arzikin muhalli a cikin tsarin kasa na cigaba. A cewarsa, kididdigar arzikin muhalli ba wani aiki na dole ba, amma wani ginshikin arzikin kasashe ne da bisan shi za'a iyar gina zaman al'umma mai karko, cikin daidaici da samun alfanu, in ji mista Steiner a yayin wani taron kasa da kasa a birnin Nairobi na Kenya.

Jami'in ya jaddada cewa, dimbin albarlatun mahalli da Afrika take da su, in dai ana kulawa da su yadda ya kamata, to za su iyar gaggauta kawo sauyi ga zaman al'umma da tattalin arzikin nahiyar Afrika.

Hukumar kula da muhalli ta MDD PNUE, a cikin wasu rahotonninta na baya baya, ta jaddada cewa, cigaba mai karko a Afrika na dogaro da yadda ake ba da kulawa ga yawan arzikin muhallinta.

Afrika na taka muhimmiyar rawa a halin yanzu ta fuskar kulawa da albarkatun muhalli, domin har yanzu Afrika na mallakar albarkatun muhalli masu tarin yawa wadanda a wannan lokacin da muke ciki ake rasa su a wasu sassan duniya, in ji wannan jami'i.

Ministoci, kwararru da masu fada a ji daga kasashen Afrika sun halarci taron Nairobi kan batun bunkasa aikin kimanta arzikin muhallin domin ingiza cigaban dake tafiya ba tare da gurbata mullahi ba a nahiyar Afrika. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China