in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 71 suka mutu sama da guda 100 suka jikkata a fashewar bam din da ya auku a Najeriya
2014-04-14 20:31:07 cri
Rahotanni daga Najeriya na cewa akalla mutane 71 aka tabbatar da sun halaka sannan wadansu 124 suka raunana a sakamakon fashewar Bam din sanyin safiyar litinin din nan daya auku a tashar motar Nyanya a wajen babban birnin Tarayyar kasar Abuja.

Manzo Ezekeil Kakakin Ma'akatar bada agajin gaggawa na kasar NEMA yace wadanda suka jikkata an garzaya dasu asibitoci daban daban don samun magani.

Wani wanda hakan ya faru akan idon shi yace wani abu ya fashe a cikin wannan tashar motar dake makare da jama'a da suka fito fara hada hadar ranan. (Fatimah Jibril )

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China