A cewarsa, kwamitin zabe na kasa mai zaman kansa INEC zai baiwa dukkan mutanen da suka cancanci zabe da kuma aka ma rajista damar samun katunansu kafin zaben gama gari a shekarar mai zuwa.
Zarraba katunan zai fara a dukkan fadin kasar tsakanin watan Mayu da Satumba na wannan shekara.
Kuma kafin rarraba katunan zabe, za'a ci gaba da yin rajistan masu zabe domin wadannan shekarunsu suka kai 18 damar yin rajista da yin zabe, in ji mista Jega.
Babban jami'in ya jaddada makasudin gudanar da zabubukan cikin adalci da 'yanci a shekara mai zuwa, tare da bayyana cewa shirin wadannan zabubuka zai kasance mafi kyau daga cikin zabubukan da aka shirya kasar.
Zabubukan shekarar 2011 an yi su cikin tashe tashen hankali da suka barke a jihar Kaduna dake arewa maso yammacin kasar da kuma suka haddasa mutuwar mutane a kalla goma. (Maman Ada)