in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jama'ar Ukraine sun nuna adawa ga daukar matakan soji a gabashin kasar
2014-04-17 15:54:50 cri

Daukar matakan soji da gwamnatin kasar Ukraine ta fara aiwatarwa musamman game da batun yaki da ta'addanci a gabashin kasar, ya haifar da rashin jituwa tsakanin sojoji da dakarun sa kai a biranen Slaviyansk, da Kramatorsk na jihar Donetsk. Lamarin da ya janyo musayar wuta a wasu wurare.

Ma'aikatar tsaron kasar Ukraine ta tabbatar da cewa, a ranar 16 ga wata wasu dakarun sa kai sun kame motoci masu sulki guda 6 na sojojin kasar, wadanda ke gudanar da aikin musamman na yaki da ta'addanci.

Bayan kame motocin an tuka su zuwa birnin Slaviyansk, inda aka ajiye su a wani babban fili da ke dab da babban ginin majalisar dokoki, inda dakarun da ke sanye da tufafin sojoji, sun kuma rufe fuskkokin su rike da makamai ke lura da su.

Wani wanda ya yi ikirarin cewa shi mamba ne na dakarun kungiyar 'yantar da Donbass ya gaya wa wakilinmu cewa,

'Wadannan motoci mun kwace su ne daga sojojin kasar Ukraine. Mun mayar da su hannun mu lami lafiya, ba a samu wani hargitsi yayin hakan ba. Lokacin da sojojin Ukraine suke zirga-zirga a birnin mu, sun gano cewa fararen hula ne ke zama a nan, don haka sun san cewa babu bukatar yaki.'

Duk dai da cewa daukar matakin da gwamnatin kasar Ukraine ta yi, na sanar da kaddamar da aikin musamman na yaki da ta'addanci a birnin Kramatorsk, da ke dab da Slaviyansk, sojoji sun fafata da dakarun sa kai, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane, tare da jikatar wasu. A hannu guda a ranar 16 ga watan nan, yayin da wakilinmu ya ziyarci birnin na Slaviyansk, ya ga tsofaffi, da yara suna gudanar da harkokinsu na yau da kullum, ba tare da wata matsala ba. Yayin da suke bayyana halin da ake ciki a yanzu, wasu mazauna wurin sun ce.

'Ni kaina, na goyi bayan kasar mahaifiyata, wurin da aka haife ni, inda na girma, kuma inda zan gudanar da ragowar rayuwata. A nan wuri ne kuma, na reni yarana, har suka girma. Ina fatan ci gaba da zama a kasar Ukraine, bana fatan ta samu baraka, da Allah al'umma ina kirammu da mu kiyaye cikakken yankin kasa, don kada jama'a su fada halin firgici, yadda kuma za su iya bayyana ra'ayoyinsu cikin 'yanci.'

Wata daliba daga sashen nazarin tunanin bil'adama a Jami'ar horas da malamai ta gwamnatin Donbass ta gaya wa wakilinmu cewa,

'Muna zaune a kasarmu, muna tsaya tsayin daka kan matsayinmu, ba ma sa hannu a cikin harkokin sauran kasashe, wannan shi ne abun da ya fi muhimmanci. Muna damuwa da makomarmu, a matsayin mu na matasa, yawancinmu muna goyon bayan kada kuria'ar raba gardama.'

A birnin Donetsk, wasu jama'a sun taru a gabannin babban ginin gwamnatin, inda masu zanga-zanga da ke goyon bayan Rasha suka mamaye, koda yake babu wani tashin hankali da ya auku sakamakon hakan. Game da aikin musamman na yaki da ta'addanci da gwamnatin take gudanarwa a gabashin kasar Ukraine, wani mazaunin birnin Donetsk ya ce,

'Ina dalilin da ya sa gwamnati ta dauki matakin soja kan jama'a? Suwa ye gwamnatin za ta yaka? Mu ne? 'Yan uwansu ko kakaninsu za su yaka? Wannan ba wai ra'ayina ba ne ni kadai, gaskiya ce a zahiri. Kawai dai suna bin umurnin Amurkawa ne.' (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China