Bisa goron gayyata, Wu ta yi jawabinta a jami'ar George Mason ta Amurka kan kafa sabuwar dangantaka tsakanin Sin da Amurka, inda ta jaddada cewa, tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Asiya da tekun Pasifik ya dace da moriyar Sin da ta Amurka, da ma duk sauran kasashen dake wannan yanki. Batun tekun Gabas da Kudu ya shafi ikon mallakar kasar Sin da ikon mallakar tekun kasar. Ana fatan Amurka za ta daidaita wannan batu cikin adalci. Sau da yawa Amurka ta taba bayyana cewa, za ta dauki matsayin ba ruwanta kan wannan batu, amma wasu bayanan da jami'an Amurka suka yi a kwanan baya sun saba wa wannan matsayi a fili, suna ba da goyon baya ga Philippines, tare da kwatanta daukar wannan batu a matsayinda irin batun Ukraine, tare gami da tura sakwannin kawo rudani ga duniya.
Dadin dadawa, Wu ta kara da cewa, jami'an Amurka sun kyale abubuwan dake cikin sanarwar ayyukan bangarori daban daban dake yankin tekun Kudu, tare da bullo da wasu da ba su cikin wannan sanarwa. Wu ta yi nuni da cewa, a cikin sanarwar, ba a yarda da a ba da abinci ko kafa gidaje a tsibirin da aka mamaye ba bisa doka ba. A maimakon haka, an tanadi cewa, kamata ya yi a daidaita wannan batu ta hanyar yin shawarwari cikin lumana. Idan Amurka tana fatan tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan yanki, kamata ya yi ta cika alkawarinta, musamman ma ta daina gabatar da bayanai irin na rashin hankali, domin da dakatar da bada goyon baya ga wasu kasashen da suke yin barazanakokarin tsokana da ta da rikici.(Fatima)