140408-murtala.m4a
|
Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Najeriya, Farfesa Attahiru Jega, ya ce hukumarsa za ta sanya ido da binciken kan inda jam'iyyu suke samun kudaden da za su yi amfani da su wajen yakin neman zabe a shekarar 2015.
Farfesa Jega ya bayyana hakan ne a jiyar ranar Litinin a Abuja, inda ya ce hukumarsa kuma za ta sanya ido kan kudaden da 'yan takara za su yi amfani da su.
Sa'an nan ya ce hukumar za ta yi hadin gwiwa da kungiyoyi masu zaman kansu don samun nasarar cimma wannan burin da ta sanya a gabanta.
Game da gudanar da zabukan shekarar 2015 a rana guda kuma, Farfesa Attahiru Jega ya ce ba ya tunanin hukumar a wannan lokaci za ta shirya yin hakan.
"Muna kokwanton gudanar da zabukan shekarar 2015 a rana guda, sai dai muna tunanin tsara hakan a nan gaba. A wajen hukumar mu ta INEC ba mu yi imanin za mu iya gudanar da hakan ba a shekara ta 2015" in ji Farfesan.
A cewar shugaban INEC, akwai wahalhalu da sarkakiya wajen shirya zabukan rana guda, saboda ba za'a iya kwatanta Najeriya da kasashe irin su Kenya da Ghana ba, inda aka gudanar da zabukan baya-baya a kasashen a ranaku guda.
Haka kuma ya jaddada cewa ba'a tsara jadawalin zabukan shekarar 2015 domin taimakawa ko bada fifiko ga wata jam'iyya ko wani dan takara ba, kamar yadda wasu suke ikirarin cewa hakan ka iyar faruwa.(Murtala)