A cewar hukumar binciken yanayin karkashin kasa ta kasar Amurka, girgizar kasar ta auku ne da misalin karfe 8 da 'yan mintuna a daren ranar Asabar bisa agogon GMT. Jim kadan da hakan kuma wata girgizar kasar mai karfin maki 7.6 ta sake aukuwa kusa da wannan wuri.
Zuwa yanzu ba a samun cikakken bayani kan hasarar da bala'in ya haddasa ba.
Tuni dai hukumar ba da gargadi kan abkuwar bala'in ambaliyar ruwa ta Tsunami a tekun Pacific, ta tunasar da kasashe 3 da suka kunshi tsibiran Solomon, da Vanuatu, da Papua New Guinea, kan yiwuwar aukuwar ambaliyar Tsunami a sassan wadannan kasashe, sakamakon waccan girgizar kasa da ta abku a ranar Asabar. (Bello Wang)