A cikin wata sanarwa da hukumar abincin ta bayar a jiya Alhamis, Hukumar ta majalisar dinikin duniya, wacce ke da hedkwata a birnin Rome, ta ce mutane fiye da miliyan ukku ne ke fama da matsalar karancin abinci, a inda kuma akwai yiwuwa, adadin jama'ar na iya karuwa su kai miliyan hudu a watanni masu zuwa, saboda dalilai da suka hada da karin tashe-tashen hankula, karuwar wadanda ke rasa muhalansu a Darfur, da kuma matsalar jerangiya na 'yan gudun hijira daga makwabtaciyar kasa ta Sudan ta Kudu.
Hakazalika sanarwar ta ce sauran matsalolin sun hada da rashin samun albarkar amfanin gona da kuma rashin tabbas na farashin abinci.
Sanarawar da Hukumar samar da abincin ta majalisar dinkin duniya ta fitar, ta ci gaba da cewa a wasu sassa na Sudan ana sa ran matsalar abincin da ake fama da ita a yanzu za ta yi kamari, nan da 'yan makonni, ya zuwa wani hali na neman agajin gaggawa, shiga irin wannan yanayin zai haifar da kara yawan matsalar da ake fama da ita a yanzu na karancin abinci mai gina jiki,wanda hakan zai jefa talakawa cikin wani mawuyacin hali. (Suwaiba)