Kwamitin kiyaye hakkin dan Adam ya shirya zaman taron musamman karo na 20 a birnin Geneva a wannan rana, don tattauna matsalar kiyaye hakkin dan Adam a Afrika ta tsakiya. A cikin wasikar da sakatare janar na M.D.D. Ban ki-moon ya aika, ya ce, Afrika ta tsakiya ta tsunduma cikin wani mawuyacin hali, ya kamata kasashen duniya sun mayar da martani cikin lokaci kan wannan tashin hankali, tare da yin kira ga bangarorin da abin ya shafa da su daina tashe-tashen hankali nan take.
A wannan rana, wakilan kasashe da kungiyoyin kasa da kasa sama da 100 sun yi jawabi a gun taron, inda suka nuna damuwa sosai game da halin da ake ciki a a wannan kasa, tare da yin Allah-wadai da tashe-tashen hankali da dakarun suka aikata wa kan jama'a, tare da fatan ganin an gaggauta farfado da zaman lafiya da karko a kasar Afrika ta tsakiya.
Rikici yayi kamari tsakanin dakarun Seleka da suka hambarar da tsohon shugaban kasar Francois Bozizé Yangouvonda da dakarun da ke sassa daban daban na kasar. Bisa kididdigar da M.D.D. ta bayar, an ce, rikicin Afrika ta Tsakiya ya sa daruruwan jama'a barin kasar kuma mutane fiye da miliyan biyu suke bukatar agajin cikin gaggawa.(Bako)