Ma'aikatar kiwon lafiya ta Guinee da ta fitar da sabon labari ta bayyana cewa adadin kamuwa da cutar na kusan kashi 63 cikin 100.
Cutar ta rarrabu kamar haka, Gueckedou an gano mutum 80 yayin 58 suka mutu, Macenta mutum 26 yayin da 14 suka mutu, Kissidougou mutane 9 yayin da 5 suka mutu.
Sannan Conakry, babban birnin kasar inda aka gano mutane 15 yayin 4 suka mutu. Haka yankuna dake tsakiyar Guinee wadanda suka hada Dabola an samu mutum 3 yayin da 2 suka mutu, sai kuma Dinguiraye mai mutum guda da mutuwa daya.
Binciken kwayoyin wannan cuta a dakunan bincike ya tattabar da nau'in cutar Ebola 35, in ji ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Guinee.
Bisa kokarin kawar da annoba, an dauki matakai da dama da suka hada da kafa cibiyoyin kebe masu jinya a yankunan da cutar ta fi kamari, sanya magani a gidajen mutanen da cutar ta kashe, bullo da hanyoyin fuskantar wannan annoba, samar da kudade, aike wa da kayayyaki kariya na mutum daya daya da rarraba jakar kayayyakin rigakafi a yankunan da cutar ta shafa.
Haka ma asusun kula da yara kanana na MDD wato UNICEF shi ma ya fara rarraba jakar kayayyakin tsabta a cikin makarantun dake yankunan da cutar shafa. (Maman Ada)