Taron ministocin kudi da na raya tattalin arziki na kasashen Afirka baki daya karo na 7, an fara shi ne a ranar 25 ga wata a otel din Transcorp Hilton dake birnin Abuja, kuma ana sa ran za'a kammala shi a ranar 30 ga wata. Hukumomi daban-daban daga nahiyar Afrika da na kasa da kasa sun hada kansu domin shirya wannan taro, ciki har da kungiyar tarayyar Afirka AU, kungiyar kula da shirin abinci ta MDD wato WFP, da kuma kwamitin kula da tattalin arzikin Afirka na MDD.
Ministocin kudi da na tattalin arziki na kasashen Afirka da yawa sun halarci taron, a bangaren Najeriya, akwai ministar kudi Dr. Ngozi Okonjo Iweala, da dai sauran wasu manyan jami'an gwamnatin kasar da dama.
Malam Salisu Dambatta, wanda shi ne shugaban kwamitin mu'amala da 'yan jarida dangane da wannan taro, ya yi takaitaccen bayani game da muhimman batutuwan da ake tattaunawa a gun taron.
A nata bangaren kuma, Dr. Kaffa Jackou Rakiatou Christelle, karamar ministar bunkasa masana'antu ta Jamhuriyar Nijar wadda ta zo nan Abuja takanas domin halartar taron ministocin kudi da na raya tattalin arziki na kasashen Afirka, ta bayyana ra'ayinta dangane da muhimmiyar rawar da Nijar ke takawa a fannin bunkasa tattalin arziki da masana'antu.
Haka kuma wajen taron an gudanar da wani karamin taron sanin makamar aiki dangane da hanyoyin da za'a bi domin kawar da matsalar tamowa da rashin abinci mai gina jiki da yara ke fuskanta a Afirka. Hajiya Amina Muhammed, wadda ita ce mataimakiyar sakatare-janar na MDD Ban Ki-Moon a kan harkokijn jama'a, ta bayyana matukar muhimmancin taimakawa yara masu fama da matsalar yunwa da tamowa. (Murtala Zhang)