Gamayyar jamai'an tsaro da suka hada da 'Yan sandan kwantar da tarzoma,da sauran jami'ai masu farin kaya sun tare hanyoyi da zai je zuwa ga cibiyar,inji wata majiya data shaida ma Xinhua.
Su dai wadanda ake tsare da su sunyi kokarin guduwa ne daga inda suke zaman jarun a harabar hukumar a safiyar lahadi lokacin da ma'aikatan dake kula da wajen suka je kai masu abinci in ji kakakin hukumar leken asiri ta kasar Marylyn Ogar, wanda kuma a nan take aka yi dauki ba dadi da jami'an tsaron wajen, abin da yayi sanadiyar kashe wadanda ake tsare da su su 18. (Fatimah Jibril)