in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Isra'ila ya bayyana farfado da tattaunawar zaman lafiya a matsayin wata babbar dama
2013-07-22 10:58:24 cri
A ranar Lahadi ne shugaban Isra'ila Simon Peres ya bayyana cewa, sake farfado da tattaunawar zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Palasdinawa, za ta kasance wata muhimmiyar dama ga bangarorin biyu.

Wata sanarwar da fadar shugaban kasar ta Isra'ila ta bayar, ta ambato shugaban yana cewa, "koda ya ke na san cewa, za a fuskanci wasu matsaloli, amma dukkanmu ba mu da wani zabi a wannan karon."

Shugaban ya ce, "Galibin al'ummomin bangarorin biyu, suna goyon bayan samun zaman lafiya, kuma abu ne da ake matukar bukata, akwai wadanda ba su fahimci al'amarin ba, amma yanayin a wannan karon, ya sha bamban da na baya"

Shugaba Peres ya yaba kokarin wadanda suka sake farfado da shawarwarin, inda ya fara yabawa shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas, mutumin da ya kira a matsayin abokinsa, kana wanda ya yi imanin zai kasance uba ga sabuwar kasar Palasdinu ta zamani.

A ranar Jumma'a da yamma ne, sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry wanda ya ziyarci yankin sau 6 cikin watanni 4, domin ciyar da tattaunawar zaman lafiya gaba, ya bayar da sanarwar cewa, jami'an sassan biyu wato Israi'ila da Palasdinu sun amince su sake fara tattaunawa a tsakaninsu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China