140326murtala
|
Kungiyar gwamnonin arewacin Najeriya, karkashin jagorancin gwamna Babangida Aliyu na jihar Neja, ta gudanar da wani taron gaggauwa, taron da ya fi maida hankali kan babban taron kasar da ake gudanarwa yanzu haka a babban birnin tarayyar kasar Abuja.
Gwamnonin sun yi zaman ne domin tattaunawa, da fidda matsaya kan irin bukatun da suke son wakilan su, su gabatar a zauren taron.
Har wa yau kuma gwamnonin sun nemi babban taron ya sake yin nazari kan yadda ake rabon arzikin kasa, da kuma duba matsalar tabarbarewar yanayin tsaro a kasar nan, musamman ma yankin arewa maso gabas, don zakulo hanyoyin magance matsalolin.
Bugu da kari a yayin taron, kungiyar gwamnonin ta karbi rahoton gwamnonin yankin 13, wadanda suka ziyarci kasar Amurka, inda suka halarci wani taro na kwanaki uku kan matsalolin yankin, taron da kasar Amurkar, da hadin-gwiwar kasashen Denmark da Norway suka shirya.(Murtala)