in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta gabatar da shawarwari hudu don sa kaimi ga yin shawarwari a tsakanin Palesdinu da Isra'ila
2013-06-18 21:05:08 cri
A gun taron kasa da kasa na goyon bayan shimfida zaman lafiya a tsakanin Palesdinu da Isra'ila da aka gudanar a ranar 18 ga wata a nan birnin Beijing, mai bada taimako ga ministan harkokin waje na kasar Sin Ma Zhaoxu ya gabatar da shawarwari hudu, inda ya yi kira ga kasa da kasa da su fahimci muhimmanci na warware batun Palesdinu, da kara yin hadin gwiwa da samun fasahohi don sa kaimi ga sake yin shawarwari a tsakanin Palesdinu da Isra'ila.

Ma Zhaoxu ya bayyana cewa, muddin ana bukatar warware batun Palesdinu, kamata ya yi a aiwatar da shirin da kasashen biyu suka cimma ta hanyar yin shawarwari cikin lumana. Kafa kasar Paledinu hakki ne na jama'ar Palesdinu, kana shi ne abu mafi muhimmanci wajen warware batun Palesdinu. Ya kamata a warware batun ta hanyoyin yin shawarwarin siyasa da kuma kyautata rayuwar jama'a. Kana Ma ya yi kira ga kasa da kasa da su kara yin hadin gwiwa tare da kasar Palesdinu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China