Li Keqiang ya kara da cewa, sabuwar gwamnatin kasar Sin tana mai da hankalinta sosai wajen karfafawa da kuma bunkasa huldar hadin gwiwa irin ta sada zamunta tsakanin kasar Sin da Palesdinu, kuma tana tsayawa tsayin daka kan matsayin nuna goyon baya ga gwagwarmayar neman adalci da jama'ar Palesdinu suke yi.
A nasa bangaren, malam Mahmoud Abbas ya ce, bangaren Palesdinu yana son kara bunkasa hadin gwiwar moriyar juna tsakaninta da kasar Sin, kuma tana maraba da kamfanonin kasar Sin da su zuba jari a Palesdinu. Bugu da kari, malam Abbas ya ce, bangaren Palesdinu na fatan kasar Sin za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa a kokarin kawo zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya. (Sanusi Chen)