Hukumar wasan kwallon kafar ta kasar Holland dai ta sanar a ranar 28 ga watan nan, cewa Guus Hiddink, zai maye gurbin Louis van Gaal mai shekaru 62 a duniya, a matsayin sabon kocin kungiyar kwallon kafar kasar ta Holland, bayan gasar cin kofin duniya ta bana. Sai dai van Gaal ba zai yi rataya ba ne, canza wurin aiki ne kawai yake nema.
A watan Disambar bara ne dai Hotspur ta rattaba hannu kan wata kwangila da kocin ta Tim Sherwood ta tsawon watanni 18, sai dai gazawar kungiyar ta samun damar shiga gasar zakarun turai ta UEFA, ya sa za a karbe wannan aiki daga Sherwood kafin wa'adinsa ya cika.
Ruud Gullit ya shaidawa manema labaru cewa, darekatan kulob din Hotspur Daniel Levi ya taba zuwa gidan Louis van Gaal, don haka a ganinsa tabbas ne an gayyaci van Gaal don ya jagoranci kulaf din na Hotspur.
Game da wannan ci gaba, van Gaal ya ce, yana fatan shiga tsarin gasar Premier, don haka zai yiwu ya karbi aikin horas da 'yan wasan kulaf din na Hotspur.
Bisa tarihin aikin sa, Louis van Gaal ya taba jagorantar kulaflikan Ajax, da Barcelona, da Alkmaar, da FC Bayern Munich, amma bai taba buga gasar FA Premier ba. Yayin da shi kuwa a nasa bangare kocin dake shirin barin kulaf din na Hotspur Sherwood, a baya ya jagoranci Hotspur din a gasanni 21 da suka buga, inda suka samu nasara a wasanni 10, aka ci su wasanni 8, tare da buga kunnen doki sau 3. (Amina)