Wannan fili da a da aka yi wa lakabi da "Filin wasan Rome" za a canja sunansa, bayan da wani kamfani ya zuba jari cikin aikin sa. Yawan kudin da filin zai lashe ya kai Euro miliyan 300, banda Karin wasu kudaden da za a bukata, idan har za a gina wasu manyan kayayyaki, da hanyoyi a kewayensa. An kuma ce kungiyoyi masu zaman kansu ne za su zuba jarin. Haka nan bisa bayanan da kulaf din na Roma ya fitar sabon filin wasan dake da kujeru dubu 52 da dari 5, za a iya fadada shi zuwa kujeru dubu 60 idan akwai bukatar hakan.
Za dai a gina wannan fili ne a Kudu maso Yammacin birnin Rome, a wani wuri mai tazara kadan daga tsakiyar birnin, da kuma filin saukar jiragen sama na Fiumicino. Za a kuma iya yin amfani da shi nan da shekarar 2016 ko 2017. Kulaflikan Rome da Lazio dai na amfani ne da filin wasan motsa jiki na Olympic dake Rome, tuni kuma shugaban birnin Rome ya goyi bayan ginin sabon fili da ake shirin farawa. (Amina)