Yayin wasan da aka buga a filin wasan AC Milan na San Siro, a ci gaba da buga gasar cin kofin kalubale na kasar Italia Serie A, Mario Balotelli ne ya fara bude saka kwallo a raga, sai kuma kwallaye Biyu da Kaka ya zura a ragar Chievon. Wannan nasara da AC Milan ya samu ta bashi damar lashe wasanni Biyu a jere, matakin da ya sauya rashin nasara a wasanni Hudu a jere da kulaf din ya fuskanta a baya.
Seedorf ya ce ya zo da sabon tsarin buga wasa, wanda zai dau lokaci kafin 'yan wasa su saba da shi, amma daga karshe za a samu nasarar da ake fata. " A hankali 'yan wasa na, na lakantar salon daidaita tsakiyar su, suna iya kare wannan daidaito da hadin gwiwar sauran 'yan wasa baki daya" A kalaman Seedorf.
Seedorf wanda ya zayyana dalilan rashin nasarar su, a wasannin baya baya da suka buga da kulaflikan Juventus, da Atletico Madrid, da Napoli, da ma wasan su da Parma, ya kara da cewa, sannu a hankali salon da suka dauka zai kai su ga cimma nasarar da suke fata. (Saminu Alhassan)