in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Barcelona ya baiwa mai tsaron gida Valdes damar tsawaita kwantiragin sa
2014-03-31 18:00:13 cri
Shugaban kulaf din kwallon kafar Barcelona Josep Maria Bartomeu ya bayyana cewa, damar kulaf din a bude take, ga mai tsaron gidan ta Victor Valdes, ta tsawaita kwantiragin sa da kulaf din, duk kuwa da raunin da ya ji a Larabar da ta gabata. Raunin da zai hana shi buga wasa har tsahon watanni 6 nan gaba.

Valdes wanda ya samu rauni a kokon gwiwarsa ta dama, yayin wasan da Bacan ta lallasa Celta Vigo da ci 3 da nema, na daf da kare kwantiraginsa da kulaf din cikin watan Yunin dake tafe. Sai dai wannan rauni zai hana shi shiga a dama da shi a wasannin karshen gasannin wannan kaka da ake bugawa, da gasar cin kofin duniya dake tafe, da ma wasannin farko farkon kakar wasannin shekarar badi.

A baya dai Valdes, ya taba bayyana fatan sa na kammala kwallo a wani kulaf na daban ba Barcelona ba, an kuma ce kulaf din Manchester City na zawarcin sa, duk da hakan dai Bartomeu ya ce Bacalona ba za ta bar shi haka ba. Kulaf din zai yi farin ciki idan har ya amince ya tsawaita zaman sa a Baca.

"Muna lura da yanayin da yake ciki, kuma bani da wata masaniya ta shirin komawar sa wani kulaf na daban, kuma shi ma ya san za mu yi farin ciki, muddin ya amince da bukatar mu ta ya zauna da mu" A kalaman Bartomeu, yayin zantawar sa gidan Radion Cadena Cope na kasar Sifaniya.

A daya hannu kuma Bartomeu ya tabo batun kocin kungiyar Gerardo 'Tata' Martino, wanda a baya bayan nan ake ta cece-kuce kan makomar sa a kulaf din na Baca, sakamakon rashin samun cikakkiyar nasarar da ake zato daga gare shi a baya. Koda yake dai nasarar da kulaf din ya samu kan Real Madrid a karshen mako ta daga matsayin kocin a halin yanzu.

Bisa kwantiragin da sassan Biyu suka sanyawa hannu, Tata zai kammala aikin sa a kulaf din ne a shekarar 2015 mai zuwa, koda yake sassan na da ikon dakatar da kwantiragin kafin cikar wa'adin idan har basu gamsu da yadda lamaura ke gudana ba. Don gane da hakan ne ma Bartomeu ke cewa, a yanzu dai sun yaba da aikin kocin. Ganin yadda kwatsam ba tare da wani shiri ba ya karbi ragamar kulf din daga tsohon kocin kungiyar Tito Vilanova, wanda ke fama da ciwon sankara. Hakan a cewar Bartomeu abun a yaba ne, don haka Baca ke yabawa da aikin Martino.

Bartomeu ya kara da cewa yanzu haka kulaf din na samun irin nasarar da dukkannin mai kaunar sa ke fatan gani.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China