in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dan wasan Bayern Munich Thiago Alcantara ba zai buga ragowar wasannin kakar bana ba
2014-03-31 18:01:02 cri
Rahotanni daga mahukuntan kulaf din Bayern Munich na kasar Jamus na cewa, dan wasan tsakiyar kungiyar Thiago Alcantara, ba zai iya buga ragowar wasannin da za a buga a kakar wasannin da ke daf da karewa ba, sakamakon raunin da ya ji a gwiwarsa ta dama, yayin wasan da kulaf din ya buga da Hoffenheim. An ce Alcantara zai yi zaman jiyyar makwanni 6 zuwa 8.

Wannan dai hali da Alcantara ya shiga, zai hana shi buga wasannin quarterfinals, a gasar cin kofin zakarun turai, inda Bayern za ta fafata da Manchester United. Tuni dai kocin kungiyar Pep Guardiola ya bayyana hakan da babban abun damuwa, wanda yace ya zowa kungiyar a wani lokaci mawuyaci.

Alcantara mai shekaru 22 da haihuwa, ya fara bugawa Bayern wasa ne a kakar 2013, ya kuma ci wa kulaf din kwallaye 2 cikin wasanni 16 da ya buga. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China