in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya kai ziyara ga matasa 'yan wasan kwallon kafa na Sin dake samun horo a Jamus
2014-03-31 17:58:57 cri

A ranar Asabar 29 ga watan Maris, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyara birnin Berlin, domin ganawa da matasa 'yan wasan kwallon kafar Sin, wadanda suke samun horo a kasar Jamus.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa filin wasa na Olympia dake birnin Berlin da safiyar ranar Asabar, inda matasa 'yan wasan kwallon kafa su 20 daga gundumar Zhidan, ta lardin Shaanxi na nan kasar Sin suke samun horo, tare da 'yan wasa na kulob din Wolfsburg, bisa jagorancin wani mai horas da 'yan wasa dan kasar Jamus.

Shugaba Xi wanda yayin ziyarar ta sa ya kalli kwallon da Kulaflikan Biyu suka buga, ya kuma sauraron bayanai dangane da kuloflikan. Shugaba Xi ya kuma yaba da yadda 'yan wasan suka taka leda cikin managarcin yanayi.

Ziyarar da shugaban kasar ta Sin ya kaiwa wadannan 'yan wasa, tare da zantawa da su da ya yi, ya faranta ransu kwarai. Haka kuma 'yan wasan sun bayyana masa kaunarsu ga kwallon kafa, da kuma fasahohin da suka samu a Jamus. A hannu guda shi kuma shugaba Xi ya bayyana musu fatansa na cewa bayan wannan horo, za su taka rawar a zo a gani a fannin bunkasa wasannin kwallon kafa ta matasan Sin. Ya ce yana fatan da yawa da matasa za su zage damtse kan sha'anin wasan kwallon kafa. Daga nan sai ya bayyana imanisa a kan su, yana mai yakinin za su kasance kwararru a nan gaba.

Bugu da kari, shugaba Xi ya bayyana wa masu kula da kungiyoyin wasan kwallon kafar Sin da na Jamus cewa, yana fatan kasashen biyu za su karfafa mu'amala tsakaninsu a sha'anin wasan kwallon kafa. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China