in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Messi ya zama dan wasan kwallon kafa mafi yawan zura kwallo a tarihin kulob din Barcelona
2014-03-17 21:25:25 cri

Makon nan da muke ciki mako ne mai matukar muhimmanci kwarai ga Lionel Messi, da ma kulaf din da yake yiwa wasa wato Barcelona, bayan da Messi ya taimakawa Barcelona wajen lallasa Osasuna da ci 7 da nema, a wasan su na ranar Lahadin da ta gabata.

A sa'i daya kuma sakamakon wancan wasa ya sanya jimillar kwallayen da Messi ya ciwa kulob din na Barcelona kaiwa 371. Matakin da ya sanya shi zama dan wasa mafi jefawa kulaf din kwallo a daukacin tarihin sa. Yanzu haka dai Mesi ya zarce Alcantara, wanda ya taba ciwa kulaf din kwallaye 369 shekaru 87 da suka wuce.

A wasan Barca da Osasun da ya gabata dai, cikin minti 18 da farawarsa ne Sanchez Juan Ignacio, ya buga wa Messi kwallo, wadda nan take ya sanya a zaren Osasuna. Kwallon da ta zama ta farko a wannan wasa. Ana daf da tafiya hutun rabin lokaci ne kuma da taimakon Iniesta, Messi ya sake jefa kwallon sa ta Biyu. Wadda ta kasance ta 370 da Messin ya ciwa kulaf din na Barcelona. Ta kuma kawo shi ga zarta yawan kwallayen da Alcantara ya ciwa kulaf din.

Nan take kuma aka rubuta cewa "Messi ya zamo dan wasa mafi kyau a tarihin kulob din Barcelona" a babban allon dake filin wasa na Nokamp. Ana cikin minti na 88 ne kuma Alves ya sake baiwa Messi wata damar, inda nan ma ba tare da bata lokaci ba ya sanya kwallo a raga. A karshen wannan wasa na ranar Lahadi dai Messi ya samu nasarar jefa kwallaye Uku a zaren Osasuna, adadin da ya kai shi ga ciwa Barcalonan kwallaye 371.

Bisa kididdiga ya zuwa yanzu, a matsayin sa na dan wasan kulob din na Barcelona, Messi ya ci kwallaye 344 a gasannin da kulaf din ya buga 412, sai kuma kwallaye 27 da ya ci yayin wasannin sada zumunci 40. Jimillar da ta sanya yawan kwallayen na sa kaiwa ga 371 a cikin wasanni 452. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China