Tuni dai burin kulaf din na lashe wasan sa da Osasuna ya cika, bayan da a ranar Lahadin da ta gabata, kulaf din Barcelona ya lallasa Osasunan da ci 7 da nema.
Ana dai ganin wasan Baca da takwaransa na Real Madrid mai zuwa, na cikin muhimman wasanni da za a buga a kakar wasanni ta bana. Inda dole ne Barcan ta lashe wasan, muddin dai tana da burin wuce Madrid din a kokarin ta na lashe gasar La Liga ta bana.
Duk da shirin da Barcan keyi na tunkarar wasanta da Madrid, a hannu guda wasan ta da Osasunan a gida ya yi bazata, domin da an yi tsammanin kulaf din na Osasuna zai yi wani yunkurin tabuka wani abu, duba da cewa a baya ya rike Barca da Madrid kunnen doki a gida.
Yanzu haka dai Real Madrid ne ke kan gaba a teburin gasar ta La Liga da jimillar maki 70, sai kuma Atilantico Madrid dake da jimillar maki 67, yayin da Barcelona ke biye a matsayi na Uku da maki 66.(Saminu Alhassan)