in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Deco zai shigar da kara kotu
2014-03-17 21:14:41 cri
Tsohon dan wasan kasar Potugal, wanda kuma ya taba bugawa kulaf din Barcelona kwallo Anderson Luis de Souza, wanda aka fi sani da Deco, ya ce zai kai karar masu ruwa da tsaki, wajen yi masa kazafin shan kwayoyin kara kuzari gaban kuliya.

Deco wanda ya bayyana hakan ta bakin lauyan sa Marcos Motta, yace suna nazarin hanya mafi dacewa ta fuskantar wannan lamari. Wanda sakamakon sa ya sanya dan wasan kammala kwallon sa ta hanyar dakatarwar da aka yi masa, tun kafin yayi ritaya.

Wata kotun hukunta laifukan wasanni ce dai ta wanke Deco daga wancan zargi na afa kwaya, bayan da a watan Satumbar da ta gabata, aka yanke masa hukuncin dakatarwa na shekara Guda, yayin da yake bugawa kulaf din Fluminense na kasar Brazil kwallo.

Sai dai daga bisani, wasu shaidun bincike da cibiyar bincike ta birnin Lusanne dake Switzerland ta fitar, sun nuna cewa dakin gwaji na Ladetec dake birnin Rio de Janeiro, ya tafka kuskure bisa sakamakon gwajin da ya yiwa wannan dan wasa, wanda bisa la'akari da wancan sakamako ne aka dakatar da shi daga murza leda.

Kamar dai yadda wata jaridar kasar Brazil mai suna O Globo ta bayyana a ranar Asabar din da ta gabata, tuni Deco ya musanta wancan zargi da aka yi masa, na ta'ammali da kwaya, yana mai cewa sam bai taba shan wata kwaya da doka ta haramta ba. Don haka bayan wanke shi daga aikata hakan, dan wasan zai nemi a biya shi diyyar illar da wancan hukunci ya janyo masa.

Dama dai a cikin watan Agustan bara ma sai da hukumar yaki da shan kwayoyi tsakanin 'yan wasa wato WADA, ta dakatar da Ladetec daga kasancewa cibiyar da za a yi amfani da ita wajen bincike, yayin gasar Olampic da za a gudanar a birnin Rio a shekarar 2016 mai zuwa. Sakamakon rashin cika ka'idar da aka gindaya. Kafin daga bisani Ladetec din ya fidda wannan sakamako da ya jefa Deco cikin mawuyacin hali.

Ladetec dai mallakar jami'ar gwamnatin tarayyar kasar ne dake birnin Rio de Janeiro. Don haka lauyan Deco ke ganin gwamnatin kasar, da Ladetec, da ma ita kanta hukumar WADA, za su iya fuskantar tuhuma cikin karar da za su shigar.

Deco dai dake da shekaru 36 da haihuwa yana cikin 'yan wasa 9, wadanda suka samu nasarar daukar kofin zakarun turai a kulaflika Biyu, wato lokacin yana kulaf din Porto da kuma Barcelona

Ya kuma fara taka leda a kulaf din sa na karshe, wato Fluminense dake Brazil ne a shekarar 2010, inda ya tallafawa kulaf din samun sanarar lashe gasanni 2, na ajin kwararru cikin shekaru 3.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China