Nantes, ya bayyana hakan ne a ranar Juma'ar da ta gabata, yayin da yake duba barnar da aka yiwa filin wasa na Fortaleza Castelao, sakamakon wasan da shahararren mawakin nan Elton John ya gabatar a filin. A cewar Nantes dole ne masu shirya irin wadannan bukukuwa su dakata, har sai an kammala wasannin gasar cin kofin duniya tukuna.
Ya ce aikin kwamitin ne ya dauki matakan da suka dace na kaucewa aukuwar matsaloli, ya kuma bada shawarwari ga masu lura da filayen, kan yadda za su kiyaye nagartar filayen.
Wannan dai shawara ko umarni na Nantes, na zuwa ne daidai lokacin da mahukuntan filin wasan Castelao dake jihar Ceara suka ayyana cewa, wani shahararren mawaki dan kasar ta Brazil mai suna Roberto Carlos, zai cashe a filin birnin a ranar 5 ga watan Afirilun dake tafe.(Saminu Alhassan)