Dr. Sufi ya ce hukumar ta kuma gurfanar da wani mabaraci a gaban kuliya, saboda karya wannan doka da yayi, ya ci gaba da yawon bararsa.
Ya ce kotun ta yanke wa wannan mabaraci hukuncin dauri na tsawon watanni uku a gidan yari, ko kuma ya biya tarar naira dubu goma.
Sa'annan Darakta-Janar na hukumar ta Hisbah ya kara da cewa, a makon da ya gabata, kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa don ganin an kiyaye dokar, ya yi nasarar kama wasu mabarata, wadanda a cewarsa 10 daga cikin su 'yan asalin jihar Jigawa ne, 15 kuma daga jihar Katsina, yayin da 8 suka fito daga jihar Kaduna.
"Dukkansu yanzu haka suna hanyar komawa jihohinsu, za mu damka su a hannun sakatarorin gwamnatocin jihohinsu", in ji Sufi.
Haka kuma ya ce akwai masu tabin hankali guda bakwai da aka kama, wadanda a yanzu haka suke a asibitin mahaukata na Dorayi, domin ba su kulawa da duba lafiyarsu.(Murtala)