140320murtala.m4a
|
Mai Shari'a Zainab Bulkachuwa za ta shugabanci kotu mai daraja ta biyu a kasar, wanda hakan zai sa a lokaci guda mata ke jagorantar manyan kotunan kasar nan mafiya daraja a karon farko.
Babbar jojin kasa, Mai Shari'a, Maryam Alooma Mukhtar, wadda ita ce mace ta farko da ta fara rike matsayin da shugaba Jonathan ya nada ta ne a shekarar 2012, yayin da duk a shekarar ya nada Zainab Bulkachuwa, mataimakiyar shugaban kotun daukaka karar, bayan murabus din Mai Shari'a Dalhatu Adamu.
Bulkachuwa wadda aka haifa a watan Maris na 1950, wakiliya ce daga jihar Gombe a kotun daukaka kara a tarayya.(Murtala)