in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kimanin mutane 55 ne suka rasa rayukansu a hadarurrukan mota daban daban a jihar Yobe ta Najeriya
2014-03-18 20:28:34 cri

Kwanan baya wasu munanan hatsuran mota da aka yi a jihar Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya, sun yi sanadiyyar rasuwar mutane akalla 55, wanda ya hada da konewar akalla mutane 19 kurmus daga cikinsu.

Daya daga cikin hadarin ya faru ne a ranar Lahadi a tsakanin Gashuwa da Garin Alkali tsakanin wata motar a-kori-kura kanta da kuma babbar mota ta daukar kaya kirar Daf, jim kadan da tashin akori kurar dake dauke da fasinjoji daga kasuwar Garin Alkali sai hadarin ya faru wanda babbar motar ta hau kan akori kurar, kuma nan take mutane sama da 20 suka rasu, 16 daga cikinsu mata ne 4 kuma maza da kuma wadanda suka ji munanan raunuka.

Hatsari na biyu kuma wanda yafi muni ya faru ne a tsakanin wata mota kirar Toyota Bus da aka fi sani da kuba ko kuma homa mai dauke da tambarin SUREP dake dauke da fasinjoji wadanda dukkan su mambobin Cocin Redeem da suka taso daga Lagos akan hanyarsu ta dawowa Damaturu a yayin da daya motar kuma kirar Golf 5 ne da ke dauke da matan da suka fito biki kusan 18 zuwa garin Potiskum, a yayin da mota ta ukun kuma ita ma kirar Golf 3 karama mai dauke da mutane 6.

Wata majiya da ke kauye Bununu da ke tsakanin Damaturu zuwa Potiskum inda hatsarin ya faru ta shaidawa cewa musabbabin faruwar hatsarin shi ne direban Toyota SUREP din ne da taso daga Lagos kasancewar yana gudu sai tayarsa ta fashe shi ne sai motar ta karkato ta afka akan motar Golf 5 suka yi taho mu gama kuma nan take Toyotar ta kama wuta a yayin da shi kuma direban Golf 3 din ya tsorota wadda hakan ne ya sa shi kuma ya kada motar tasa ya shiga daji.

Kakakin hukumar kiyaye hadarurruka ta FRSC da ke jihar Yobe Malam Yusuf Sani ya tabbatar da faruwar wadannan hadarurruka, inda ya gargadi direbobi da su gujewa halayyar nan ta gudun wuce kima.(Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China