A cikin sanarwar da kakakinsa ya gabatar, mista Ban ya bayyana damuwarsa matuka a gaban tashen tashen hankali da suka faru a ranar Jumma'a a birnin Alkahira inda mutane hudu suka mutu yayin da kusan goma suka jikkata.
Magoya bayan tsohon shugaban kasar Mohammed Morsi sun gudanar da zanga zanga da jerin gwano domin nuna adawarsu a ranar Jumma'a a yawancin manyan wuraren kasar Masar, tare da yin kira da a maido Morsi kan mukaminsa.
Birnin Alkahira ya kasance wani dandalin tashe tashen hankali masu muni tun lokacin kazamin fito na fito na watan Augusta, a yayin da magoya bayan Morsi suka yi bata kashi da masu adawa da Morsi da kuma 'yan sanda a lokacin da suke kokarin shiga dandalin Tahrir dake tsakiyar birnin Alkahira. (Maman Ada)