in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bukaci Amurka ta daina mata leken asiri
2014-03-24 20:53:16 cri
Kasar Sin ta bukaci Amurka da ta mata bayani game da leken asirin da take zargin take mata tare da gargadin ta da ta daina.

Kakakin ma'aikatan harkokin wajen ta kasar Sin Hong Lei ya sanar da hakan a yau Litinin a taron manema labarai da aka saba yi duk rana, lokacin da aka tambaye shi game da rahoton da ya bayyana cewar Amurkan na ma kasar leken asiri a kan kamfanin wayar nan ta Huawei, tsaffin shugabanninta, ma'aikatunta na gida da na kasashen waje har ma da bankunanta.

Mr Hong ya ce Sin ta damu kwarai game da rahotannin da ke nuna yaduwa, yana mai bayanin cewa kafofin yada labarai sun riga sun bayyana wassu bin kwakkwafi da binciken sirri da kuma satan bayanai da Amurka ke yi a kan wassu kasashe da suka hada da kasar Sin.

A don haka in ji kakakin ma'aikatan harkokin wajen ya ce Sin na bukatar Amurka ta yi bayani game da hakan, sannan kuma ta dakatar da irin wannan aikin. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China