Da take karin haske game da hakan ga manema labaru, Milnar ta kara da cewa akwai dan ci gaba a lissafin alkaluman kididdigar gibin dake tsakanin mazauna kauyuka da na birane a bara, wanda ya dara na shekarar 2012. Ta ce duk da kankantar wannan ci gaba, hakan ya dara matsakaicin ci gaban da OECDn ta gindaya.
A makon da ya gabata ne dai aka fidda tsarin bunkasa biranen kasar ta Sin tsakanin shekarun 2014 da 2020, wanda ya tanaji fadada birane, ta yadda kaso 60 bisa dari na al'ummar kasar za su kasance mazauna birane nan da shekara ta 2020.
Wannan adadi dai zai kasance babban ci gaba, sama da abin da bai kai kaso 54 bisa dari ba a yanzu haka. (Saminu Hassan)




