Shugabar asusun ba da lamuni na IMF Christine Legarde ce ta bayyana hakan a yau Lahadi, yayin da take jawabi gaban mahalarta taron tattauna batutuwan ci gaba da ake gudana a nan birnin Beijing.
Legarde ta kara da cewa, sauyin da kasar ta Sin ke nufin aiwatarwa ya kunshi cimma tabbatattun manufofi dake bisa managarcin tsari, tare da la'akari da bukatun kasa da kasa.
Haka zalika shugabar asusun na IMF ta bayyana sabbin tsare-tsaren da kasar ta Sin ke nufin aiwatarwa, wadanda ke kunshe cikin kudurorin da aka cimma, yayin cikakken zama na 3 na kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwamins karo na 18 a matsayin wani ginshikin cimma inganci, nagarta, da ci gaba mai dorewa a dukkanin fannonin bunkasa kasar.
Ta ce duk da kalubalen dake tattare da wannan aiki, ta yi imanin kasar ta Sin na da ikon samun tarin nasarori kamar yadda ta saba yi a baya. (Saminu Hassan)