A watan Nuwambar shekarar 2010 ne dai aka gudanar da babban zaben kasar ta Guinea, inda Alpha Condé ya lashe zaben. Sai dai an sha dage zaben majalisar dokokin kasar, wanda ya dace a gudanar watanni shida bayan babban zaben kasar, sakamakon bambanci ra'ayi tsakanin jam'iyyun adawa da jam'iyyar da ke rike da ragamar mulkin kasar.
Daga bisani bayan kokarin shiga tsakani daga kasashen duniya daban daban, a watan Yulin da ya gabata, bangarorin biyu suka daddale yarjejeniyar sulhuntawa tsakaninsu, inda suka alkawarta tabbatar gudanar zaben majalisar dokokin kasar a ranar 28 ga watan Satumba, zaben da kuma aka kammala cikin nasara.(Fatima)