Bisa taken "gina gungun gungun dangantaka", wannan dandali ya tattara jami'an gwamnati da wakilan kamfanoni da kwararru na nahiyar Afrika baki daya ta yadda zasu hada karfinsu wajen bunkasa makamashin nukiliya.
Taron ya zo a daidai lokacin da kasashen Afrika suke mai da hankali sosai wajen aiki da makamashin nukiliya. Afrika ta Kudu, Masar, Kenya da Najeriya suna shirin gina tashoshin nukiliya a cikin shekaru masu zuwa ayayin da kuma wasu kasashen Afrika suke shirin bin sahunsu ko kuma rungumar makamshin nukilya.
A cewar ministan makamashin Afrika ta Kudu, Dikobe Ben Martins, wannan dandali ya kasance wata babbar dama ga kasashen Afrika na su nuna, bunkasa da kuma tattara kwarewarsu da fasahohin nahiyar domin bunkasa tsare tsaren makamashin nukiliya.
Haka kuma taron na kwanaki uku ya taimaka wajen tabo batutuwan dake janyo hankalin jama'a wadanda suka hada tsaro, dokoki, kulawa da adanon bolar makamashin nukiliya. (Maman Ada)