Datrektan yankin Africa na kamfe din manufofin ci gaban wannann karni, Charles Abugre ya ce ana bukatar wani ginshikin matakai da zai kunshi kowa da kowa, domin ta haka ne kawai za a kai ga cimma inganta rayuwar matalauta dake nahiyar Africa.
A yayin da yake jawabi lokacin kaddamar da rahoton duniya a kan tsananin talauci, Mr. Abugre ya ce ya kamata Africa ta bullo da tsari na bai daya, wanda zai kawo canji ga rayuwar talakawa marasa galihu.
Rahoton ya ce yawan mutane dake fama da rashin ilmin zamani da kuma matsalar rauni na mulki na daga cikin abubuwan da suka haddasa yawan talauci na duniya.
Charles Abugre, ya shawarci Africa da ta mai da hankali wajen aiwatar da ci gaba a shekaru 15 masu zuwa.
Abugre ya kara da cewa a karon farko a cikin tarihi, shugabannin nahiyar ta Africa za su mai da hankali a kan ajanda guda, wacce ake sa ran za ta murkushe matsalar talauci.
Mr. Abugre ya ce cimma manufofi na kafa masana'antu gadan-gadan na daya daga cikin hanyoyin da za su dakushe talauci saboda kasancewar kafuwar masana'antu za ta haifar da guraban ayyukan yi ga jama'a.
Mr. Kwende Mwekdwa, mai kididdiga dake cibiyar bincike da kididdiga a kan manufofin gwamnati ta kasar Kenya ya bukaci Nahiyar Africa da ta aiwatar da canji a kan yadda suke tafiyar da tsare tsarensu ta yadda tatttalin arzikin nahiyar zai kaucewa dogara a kan kayayyakin da ake fitarwa zuwa kasashen ketare.
Kamar yadda ya ce, hakan zai kawo karuwar darajar ababen da ake samarwa a cikin kasashen, wannan kuma zai haifar da rayuwa mai dorewa a Africa. (Suwaiba)