Wani janar a hedkwatar ba da umurni ta sojojin kasar Afrika ta tsakiya ya bayyana cewa, a ranar 25 ga wata, wasu dakarun Seleka dauke da makamai, sun yi wa sojojin kasar Chadi kwantan bauna, yayin da suke hanyarsu ta zuwa babban filin jirgin saman birnin suka kuma bude musu wuta, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin Chadin 6, baya ga wasu sojojin kasar 2 da aka hallaka a ranar 24 ga wata.
Bisa labarin da aka bayar an ce, sojojin jama'a da dakarun Seleka sun yi taho-mu-gama a ranar 25 ga wata, kuma bangarorin biyu sun yi amfani da manyan mukamai, har yanzu, ba a tabbatar da yawan mutanen da suka rasu ba.
Yanzu haka dai akwai sojojin kasar Chadi kimanin 850 a jamhuriyar Afrika ta tsakiya, dake aikin wanzar da zaman lafiya, koda yake al'ummar kasar na nuna kyamarsu ga sojojin, wadanda suke zargi da laifin kashe jama'a da dakarun Seleka. Lamarin da ya sanya a kwanan baya, aka gudanar da wata zanga-zangar nuna adawa gare su a birnin Bangui. (Bako)