Wasu bayanai na baya-bayan nan na nuna cewa, kashi 96.6 cikin 100 na al'ummar yankin Crimea ne suka kada kuri'ar amincewa da koma wa kasar Rasha.
Hukumar shirya zaben raba gardamar yankin ta bayyana cewa, kashi 2.55 cikin 100 ne kadai suka kada kuri'ar kasancewa a Ukraine. Ko da yake sama da kashi 1.5 cikin 100 ne suka cancanci kada kuri'ar raba gardamar cikin mutane kimamin miliyan 2 na al'ummar yankin.
A cikin watan Mayun shekarar 1992 ne majalisar kolin Crimea ta ayyana 'yancin kan yankin, kafin a kada kuri'ar raba gardamar da hukumomin Ukraine din suka dakatar.
Yankin na Crimea dai ya gudanar da kuri'ar raba gardama a shekarun 1991 da kuma 1994 domin ya ji ra'ayin jama'a game da samun cikakken 'yancin kasancewa da Ukarine ko hade wa da kasar Rasha.
A ranar 6 ga watan Maris din wannan shekara ne, majalisar kolin yankin ta yanke shawarar kada kuri'ar raba gardama ta baya-bayan nan, wadda aka shirya gudanar wa a baya a ranar 30 ga watan Maris, bayan da sabuwar gwamnatin Ukraine ta yanke shawarar dakatar da amfani da harshen Rasha a hukumance a yankin. (Ibrahim)