A halin da ake ciki dai akwai murabbab'in mitoci 140,000, da ba a yi wa dakali ba, a filin wasa na Beira Rio dake Porto Alegre, wanda kawo wannan lokaci ake ci gaba da fafutukar yadda za a shawo kan matsalar kammala wannan aiki, baya ga kujerun wucin gadi da za a sanya a filin wasa na Itaquerao dake birnin Sao Paulo. Wannan dai batu ya kasance abin tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsaki a kasar ta Brazil.
Da yake tsokaci kan wannan kalubale, babban magatakardar hukumar ta FIFA Jerome Valcke, ya ce kammala wancan dakali na iya daukar watanni Biyu zuwa Uku, gashi kuma watanni Uku ne duka-duka suka rage a fara wannan gasa.
Ya ce ba wai kawai FIFA ce ke cikin damuwa ba, mahukuntan kasar Brazil, da kwamitin tsare-tsaren gasar, dama jagororin biranen da za a gudanar da gasar duka na cikin wani yanayi na damuwa.
Za dai a bude wannan gasa ne a ranar 12 ga watan Yulin dake tafe, duk kuwa da cewa akwai filayen dake biranen Sao Paulo, da Cuiaba, da Curitiba, da kawo yanzu ba a karasa aikin sanya kayayyakin da ake bukata a cikin su ba, duk kuwa da tsaida watan Disambar bara da FIFA ta yi, a matsayin wa'adin karshe na yin hakan.
Hakan a cewar Mr. Valcke abun damuwa ne, koda yake dai ana iya ci gaba da ayyukan nan da lokacin da za a bude gasar.(Saminu Alhassan)