Rivaldo ya taba kasancewa zakaran kwallon kafar nahiyar Turai, da kuma na duniya a shekarar 1999. A wancan lokacin tauraron wannan dan wasa ya haska matuka, inda ya kusa kaiwa ga shaharar da Ronaldo ya yi a fannin wasan kwallon kafa. Sai dai sabanin Ronaldo, Rivaldo ya fara neman samun 'yan kudaden shiga ne a lokutan wa'adin kwallon sa, inda da farko ya shiga kulob din Olympiacos na Greece, da kulob din AEK Athens. Kafin daga bisani ya koma kulob din Bunyodkor na Uzbekistan, da kulob din Kabuscorp na kasar Angola.
A shekarar 2012 kuma ya sake komawa Brazil. A ci gaba da buga kwallo inda Rivaldo ya shiga kulob din Mogi Mirim, wanda daga cikin sa ne kuma zai yi murabus. (Saminu Alhassan)