Rashin nasarar da Man City ya samu a wannan karo, da kuma ci 2-0 da Baca ta yi masa a zagayen farko na wasannin mako na 16 ya haifar wa masoya kulaf din da 'yan wasansa bakin ciki matuka. Ya kuma tilastawa kulaf din ficewa daga gasar ta bana. Duk da cewa Barcelona ba ta nuna wani karfi sosai kamar na baya ba, yayin wannan wasa, a hannu guda Manchester City wadda ta shahara wajen kashe kudade ta gaza samun nasarar wasannin Biyun karshe, wanda hakan zai sanya ta ci gaba da koyon darussa a wannan fage na neman nasarar wasanni.
Kyaftin din kungiyar ta Manchester city Vincent Kompany, wanda gidan telibijin na Sky Sports ya bayyana kwarewarsa, ya ce sun yi iyakacin kokarinsu a wannan karo. Ko da yake ba za a iya mantawa da wanda ya sami nasara ba, wannan ne kakar wasannin su ta Uku a gasar cin kofin zakarun turai, za kuma su sanya himma, wajen neman nasara a wasannin da zasu buga cikin wannan gasa a nan gaba.
A wasan da aka buga ranar 13 ga wata tsakanin kulaf din ParisSaint-Germain da Bayer Leverkuson a gasar cin kofin zakarun turai kuwa, PSGn ce ta lashe wasan da ci 2-1.
Wannan nasara ta baiwa PSG damar matsawa zuwa zagayen farko na wasannin quarter finals. Cikin nasarorin da kulaf din ya samu a kakar wasanni ta bana, akwai samun nasarar wasanni 28 a wasannin da ya buga a turai. Da nasarar wasanni 6 na baya bayan nan a gasar cin kofin zakarun turai. (Amina).